🌟⭐ *Imaan*⭐🌟
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
4.....
Daddy ya kalli Imaan dake goge hawayen idonta yace "Don yayanki ya debi apples kike kuka Imaan?" Ta marairaice tace "Toh daddy ai ba shi ka siyo ma ba gashi ya kwashe min gaba daya kuma wllh baya cin apple" Daddy yyi murmushi yace "Shi yace maki bai ci" cikin rawar murya tace "Ae nasan baya ci tun da can" Daddy yace "Toh anjima idan na fita xan karo maki" a hankali tace "Toh nagode" yace "Wai amma me ya hada ku da yayan naki all of a sudden Imaan" Ammi da ta fito parlon tace "I am still wondering also, lkci daya aka yi parting" Daddy yace "Ko kin masa wani abun ne dai" ta turo baki ta dawo kusa da daddy tace "Kawai dai naga ya xama mugu ne shi sa na daina kulasa" Dariya kawai daddy yayi, Ammi tace "Har nan ma ai baya shigowa yanxu" Daddy yace "Toh Allah ya kyauta" Imaan tace "Daddy ni dai ka daukan min personal driver dina plss" daddy yace "Ba Abbanku xai daukar maku driver ba, ai mun yi magana da shi bayan tsohon drivern ya wuce" Tace "A'a daddy ni dai nawa daban nake so, kilan ba yanxu driver din ma xai xo ba, yau fa Yaya bai bari na shiga motar ba don na bata masu lkci da kafata na tafi islamiyya shi sa tun da na dawo duk jikina ke ciwo sai da Ammi ta shafa min magani na kwanta da na tashi shine naji sauki"' Murmushi kawai Daddy yayi ya mike yace " Bari in yi wanka daughter " daga haka ya wuce bedroom dinsa, Ammi tace "Sai ki tashi ki kai ma Inna abinci ko yau ma baxa ki ba" Ta kalli Ammi da sauri tace "Ammi ca tayi bata son sake ganin kafata a part dinta fa, kuma in je yanxu ta gaya ma daddy" Ammi tace "Tashi ki dauki abinci ki kai mata nace" Daga haka Ammi ta bar parlon, mikewa Imaan tayi ba don ta so ba ta shiga kitchen, kusan duk abinda Ammi tayi ma daddy sai da ta dibar ma inna duk ta ajiye a basket, Imaan ta dau basket din me dauke da abincin ta fita, har ta isa part din Inna fuskarta a daure yake irin ko kulata din nan baxata yi ba, ta dinga kallon takalman dake bakin kofa kafin ta bude kofar ta shiga, Mujaheed na xaune yana kallon inna dake bada labari tayi mitsi mitsi da ido, banda murmushi babu abinda yake don da wuya yake dariya, su Maimoon da Rahma kuwa dariya har da kyakyatawa, Inna ta saita hannu sama tace "Ji kawai muka yi ratatatata.... Ba sai kakan ku ya shige karkashin gado ya bar ni da halina da 'ya yana ba, lkcn Bukar na bayana sai tsala ihu yake, Ahmadu kuwa fitsari ya dinga saki yayi sau uku a wando...." Ganin Imaan Inna tayi shiru ta jawo daya daga apples biyar dake cikin leda a gabanta ta kai baki, Har sannan su Maimoon dariya kawai suke, imaan ta ajiye basket din hannunta tana kallo chocolates din da Daddy ya kawo mata a hannunsu Maimoon, ta saci kallon Mujaheed ta juya xata fita Inna ta tabe baki tace "Ga dambun naman ki can a daki ni dai na ajiye maki bana bi ta halin ki ba" ba tare da ta juyo ba tace "Bana ci" inna na ci gaba da cin apple dinta tace "To wa yayi asara?" Mujaheed yace "Yana ina a dakin?" Da sauri Imaan ta juyo ta shige dakin, Inna tace "Ya xaka ce yana ina bayan ka ci rabon ka da wanda ma ka dauka ban baka ba" yace "Haba" tayi tsaki tace "Yana nan cikin roba xa ki gansa a rufe, duk naki ma ya fi yawa" Imaan ta fito rike da uban dambun naman da inna ta ajiye mata a bowl mai murfi ta nufi kofa, inna tace "Wannan liyafar hala Bukar ne ya dawo?" Imaan tace "Bai dawo ba" daga haka ta fita, Inna tace "Duk ta ma fige kamar bata cin abinci" Rahma tace "Mu dai ci gaba da ba mu labarin da kike yi don Allah inna" inna ta gyara xama xata ci gaba, mikewa Mujaheed yyi ya fita parlon. Imaan na komawa bangarensu ta tadda Yusuf ya shigo gaida Daddy, Ya bi ta da kallo ta boye bowl din hannunta tana wara masa manyan idanuwanta tace "Nasan ka ci naka dai" fitowar Daddy parlon yasa Yusuf bai ce mata komai ba, daddy yace "Engnr ashe kana gari" Yayi murmushi yace "Ina nan daddy, da fatan kun iso lafiya" yace "Alhmdllh My son, ya aikin fa" Yace "Mun gode Allah Daddy" daddy ya xauna kujera yace "Madalla, kowa dai lafiya koh?" Yusuf yace "Duk lafiya" Yusuf bai wani dade ba ya mike yace xai wuce, daddy yace "Baxa ka tsaya mu ci abinci ba" Yace "Alhmdllh daddy na ci abinci" Ammi dake dinning tana jera abincin tace "Anya Yaya Yusuf" dariya yayi yace "Ammi wllh na koshi" tace "Toh shikenan" sallama yyi ma daddy ya fita. Bayan magrib daddy xai je gaida inna babu yanda bai yi da Imaan su je ba ta ki, har hakan ya basa mamaki ya tafi shi kadai, inna na goge tiles din parlonta daddy ya shiga da sallama, ta mike tace "Amma dai gaskiya Bukar ka dinga kwa6a ma yar ka ta daina karya, ce min fa tayi baka dawo ba" Ya xauna yana murmushi yace "Sannu inna, ina yini" ta shimfida tabarma ta xauna tace "Lafiya lau, amma ai karya ba shi da amfani kuma a gaskiya Imaan ta iya karya" Shi dai bai ce komai ba, tace "Toh ya hanyan?" Yace "Alhmdllh mun baro hanya" tace "Wannan karan kuma kamar baxa ka sake dawowa ba" yace "Aiki ne yyi yawa Inna" tace "Toh Allah ya bada sa'a ya tsare mana ku a duk Inda kuke, ya maka albarka" yace "Ameeen inna" Tace "Toh ya xa ayi, Allah ya kaddara a can abincin ka yake, banda haka na tabbata da kana gidan nan da ka dinga share min hawaye daga bakin cikin da nake fuskanta" Daddy na kallonta da mamaki yace "Bakin ciki kuma Inna?" Inna tace "Yo bakin ciki mana Habu... Kaga yayanka baxai fito daga masallaci ya tako nan tun asuban ba ya gaisheni sai ina jin wajen karfe tara xai taho da safe ya duka can bakin kofar ya gaida ni a gurguje ya kara gaba, bana sake ganinsa Bukar sai ina kokarin kulle kofa ta da daddare shi ma Allah yasa ya yi minti biyu xaka ga yace sai da safe daga haka ya wuce, Kaga matar nan tasa Rukayya take ko wa? Uwarsu Mujaheed dai wllh kaji rantsuwar musulmi tafi wata biyu ina ga bata tako ta xo nan ta gaisheni ba sai ta gan ni a tsakar gida ko a can bangaren, ita kuma dayar mai kama da fulanin Bararoji wato Amina da suke ce ma Anty sai ta bushi iskarta xata kwaso kafafuwa ta xo gaisheni, ita wnn farar wa take da suna? Uwar wannan yarinya Imaan d'an wankin da take min da duk ta watsar sun xugeta, in kuwa wannan 'ya taka Imaan borinta ya tashi ta ki kawo min abinci to ranan fa da yunwa xan kwanta a gidan nan, Aisha ta fi karfin ta taso takanas ta kawo min da kanta, to me yafi wannan bakin ciki Yaro? Gashi gaba daya 'ya yanku sun rainani sun maida ni ba bakin komai ba, sun maida ni kakarsu tun ma ba wannan katon Mujaheed ba da ramammiyar 'yar ka, sai wannan kazamar Ummi, ni nasan da sun ga ido wllh taka ni xasu dinga yi suna wucewa, isuhu kadai ke raga min a gidan nan sai wannan yarinya Seeyama, Imaan idan ta fara balbale ni wlh shiru nake, haka ma Mujaheed yaron da aka haifa a gabana, to ina dalili ina da gata na ta ko ina don dai d'an abincin da ake yarfa min a kwano sai a maida ni bola" Daddy dake ta saurarenta ya dago kansa a karo na farko yace "Kiyi hakuri don Allah inna" a fusace tace "Na gaji da jin wnn axxalumin kalman, ayi ta baka hakuri ana cutan ka, ni dai a fita harkata, don idan tsiyata ta debeni wllh sai an fita har kasashen waje ana nemana" Daddy yace "Xa a gyara Inna, duk ki yafe masu, ita Imaan xan sameta yanxu, shi ma Mujaheed din xan gamu da shi" Tace "Atoh, sai ka xaunar da su ka tambayesu kaji ko xaman gidan ne basa son inyi, ka tambayesu dalilin da yasa basa fitsaran su a waje sai a cikin gida cikin gidan ma a kan uwarka, kayi masu jan ido ka nuna masu bacin ranka Yaro" Daddy yana murmushi yace "In sha Allah" nan suka ta6a hira amma kusan hiran gaba daya na complain ne daga karshe daddy yace mata xai wuce masallaci don an kira isha. Daddy na dawowa masallaci ya dinga kallon Imaan dake xaune parlor tana cin abinci, ya xauna yace "Imaan yanxu ita innar kika mayar abar wasar ki a gidan nan?" Kallonsa ta dinga yi kamar zata yi kuka, ya hade rai yace "would you take ur eyes off me silly girl, haka kike ma uwar ki? I warned you the last time a kan haka shine kika sake repeating foolishness din yanxu ko?" Ta sunkuyar da kanta, ya gyada kai yace "Nasan maganin ki, tashi ki bar min parlor" tashi tayi da sauri ba tare da ta bi ta kan abincin ba ta shige bedroom dinta ta kulle, ita dai Ammi bata ce komai ba, Daddy yace "I don't like this nonsense character of her, ita innar abokiyar wasanta ce, ke kuma Aisha baki taka mata burki, a kan me xata dinga rainata, I don't like that, and I am going to teach her manners soon" Ammi ta tabe baki ta mike ta dauke abincin da ta bari ta kai kitchen ta rufe, ta tsaya kitchen din tana wanke plates da ke sink. Washegari wajen karfe bakwai da rabi Imaan ta fito sanye da uniform din islamiyya, kanta a kasa ta gaida Ammi dake jera breakfast a dinning, Ammi dake kallonta tace "Wato ke ba isa a maki fada ba shine kika kwana kuka ido ya kumbura koh?" Ta fashe da kuka tace "Ni Ammi don Allah kar ki sake ce min in kai mata abinci kullum sai tayi ta ma mutum sharri alhalin ba abinda nayi mata" Ammi tace "Ko ban baki abinci kin kai ba ma da kanki naga kike kwasan kafafuwanki kije can din ko da kuwa koranki tayi" Imaan ta hade rai tace "Yesterday was the last day da xan je part dinta, har abada baxan sake xuwa ba" Ammi tace "Toh bari dai ya ji ki gashi can ya fito, ni ba ruwana" shiru Imaan tayi tana juya shayin da Ammi ta hada mata, Daddy dake tsaye parlon yace "Madam me yasa ba a kai ma Inna breakfast ne wai?" Ammi tace "Breakfast kuma?" Yace "Ehh ai ya kama ta ne" tace "A'a don Allah yallabai kar ka hada ni da ita, kullum sai Abba ya tura mata bread, tana da kayan shayi kuma tana da heater ta iya amfani da shi, meye breakfast din dama idan ba shayi da bread ba sai kwai wani lkcn, lunch da kanta tace bata so a daina kai mata wai jagwalgwalon yara ne" Tuni Daddy ya xauna ya sa news channel, Ammi ta shiga kitchen ta ci gaba da abinda take, Imaan ta gama breakfast din ta mike ta iso cikin parlor ta durkusa ta gaida Daddyn nata, sau daya ya kalleta ya amsa ya ci gaba da kallonsa, ta mike ta tafi kitchen ta amshi kudin makarantar ta gun Ammi ta fito ta dau jakarta bayan ta sa takalmi da safa tayi ma daddy sallama ba tare da ta kallesa ba ta fice daga parlon, kiranta daddy yyi ta juyo ta dawo ta sunkuyar da kanta tace "Ga ni" room freshener har biyu ya nuna mata dake ajiye yace "Dauka ki kai ma Inna kafin ku wuce" shiru tayi tana kallonsa kamar xata yi kuka, bata dai ce komai ba ta durkusa ta dauka sannan ta fita xuwa part din inna, Inna na ta goge goge bayan ta gama share ko ina fesss, banda kamshin turaren wuta babu abinda ke tashi a parlon, imaan bata kalleta ba ta ajiye abun hannunta fuska daure tace "Ina kwana" xata fita inna tace "Me ya sami idonki ni Asabe? An umaki wani abun ne" Imaan da har ta kai kofa ta juyo lkci daya ta fara kuka tace "Kawai sai kije kice ma daddy ina maki rashin kunya yaushe rabon da in xo nan...." Tana fadin haka ta fashe da matsanancin kuka, Inna da ta saki baki tace "Shine ya maki me?" Cikin kuka tace "Fada ya dinga min mana yace zai yi magani na" Inna ta dau dankwalinta ta fita parlon imaan ta bi ta da kallo tana share idonta, Ko sallama babu inna ta bude kofar parlon, daga daddy har Ammi suka daga kai suna kallonta, tace "Bukar dama yaro ba lallabasa ake yi ba a rayuwar nan, daga mun yi magana tsakanina da kai sai ka taho ka far ma yarinya da bala'i, to ae gwara ita sau dubu a kan sauran, Imaan bar ta da son jikinta amma wllh wllh bata da matsala, haka kawai ka ja mata wani cutan dama gata mai cuta iri iri kamar ta kashe d'an mutum, yanxu da kasa ta kwana tana kuka idan wani abun ya sameta me xa ka gaya ma Allah, kai dai wllh ka cika bala'i, ba haka yayanka Ahmadu yake ba, ba ruwansa da irin wannan hali, to wai ma me ta min da xafi haka da xaka sa ta kuka haka, ga abun duka can Mujaheed me nuna ni da yatsa, mai ce min Hajiya, ni tunda nake wllh xan iya kirga sau nawa Imaan ta mayar min magana shima kuma duk laifina ne....." Ammi dai tuni ta shige kitchen, Daddy kuma ya kasa cewa komai, Inna ta juya ta nufi kofa tana cewa "Wannan dai ba yi bane, kamar ba kai ka haifeta, yar gata daga ita sai ita amma kuma ka takurata, da wanne xata ji da rashin karo mata kanni da ba ayi ba har yau ko kuma da fitinar mahaifinta, kuma ka tashi ka kawo min turaren bature da ko kamshi babu wai in fesa a daki, to uwata bata ce min je ki kya gani ba turaren wuta tsadadde mai kamshi nake nufi, sai ka ba matarka mai kumewa a daki kamar matar liman ta fita kasuwa ta siyo min" daga haka ta fice ta kulle masu kofa. Dama imaan direct gun mota ta nufa bata yarda ta ma bi ta part dinsu ba. Yusuf ne ya ajiye su islamiyyar, karfe sha biyu Anty ta dauko su, A hankali Imaan ta bude kofar parlonsu tana lekan ciki, babu kowa hakan yasa ta shiga ta rufe kofar ta nufi bedroom dinta da sauri, tana kokarin cire Uniform dinta Ammi ta bude kofar, Imaan ta gaisheta kanta a kasa, Ammi tace "Amso min card waje kafin ki cire uniform din" Imaan ta amsa tana kallonta tace "Ammi daddy fa?" Ammi tace "Yana daki" Imaan ta marairaice tace "Ni fa ban gaya ma inna ya min fada ba, kawai taga idona ne haka" Ammi tace "Wannan ya rage naku ke da shi, ni kiyi sauri ki amso min card din" imaan ta maida Hijab dinta ta fita, kiosk din is just a house from theirs, ta amso card din ta juyo ta shigo gida, Umma ta gani tsaye parking space alamar xata fita, Mujaheed ya iso wajen ya bude mata back seat, sannan ya shiga driver seat, Imaan na hada ido da Umma dama ta dauke kai tayi wucewarta, Mujaheed ya bi ta da kallo ta madubi, Umma ta shiga cikin motar tace "Wllh duk ranan da ka gaida uwar yarinyar nn ko da mistake a gidan nan ban yafe maka ba Mujaheed, duk kanninka ma na karanta masu haka nasan kuma sun dauka...." Yana kallonta ta madubi yace "Haba Umma kema kin san....." Ta karasa masa da sauri tace "Baxa ka iya ba ko? tunda ga ta kanwar Ahmad ko kanwata, Mara tunani kawai da bai san ciwon uwarsa ba, to mu xuba da kai wllh, ba dai makiyana su ne mutanen arxikin ka ba a gidan nan, ka ci gaba, a ta dalilin munafukar uwar yarinyar nan na bar gidan ubanka for good 5 years, ta hade kai da kishiyata suka yi ta kulla min makirci har ubanka ya sakeni, da yake akwai sauran xamana a gidan na dawo few years back na tarar baka da masoya da ya wuce makiyana, ka maida Aisha uwarka, ka nuna duk gidan nan baka da kanwa da ya wuce yarinyar Aisha, yarinyar da bata gaisheni a ynxu ko idona xai makale a nata saboda uwar ta hanata, da kyar da siddin goshi da rokan Allah na rabaka da su, ni da ba a kan idona na haifeka ba kuma ina haihuwar ka aka ajiye min kai a gefe na da wllh bbu abinda zai sa baxan ce canjen ka aka min a asibiti ba, sam baka san mutunci na ba, ace makiyana su ne masoyan ka Mujaheed? Anya kana son gamawa lfya kuwa?" Shi dai ya kasa cewa komai, ta gyada kai ta bude motar ta fice tana cewa "Ga ka ga su ai, daga ynxu ma ka tatttara yanaka yanaka ka koma bangaren nasu" a hankali yace "Umma I have avoid a lot of things a gidan nan kema kin sani, wllh ko kadan bani son abinda xai bata maki rai, don Allah kiyi hakuri...." Ko saurarensa bata yi ba ta fice daga compound din ya sauka ya bi bayanta da sauri. Washegari har Ammi ta gama hada breakfast ta fito daga kitchen imaan bata fito daki ba, ta kalli agogo ganin bakwai da quarter ta nufi dakin ta bude ta shiga, kwance ta ganta ta dukunkune cikin bargo, Ammi ta karasa da sauri ta cire bargon tace "Are you okay Imaan?" Ta bude ido kamar xata yi kuka, Ammi ta dinga kallonta don jikinta ya dau xafi sosai, a hankali tace "Ina ke maki ciwo kuma?" Kafafuwanta ta nuna mata da kai, hawaye cike idonta tace "Ammi duka jikina ciwo, jiya ban yi bacci ba" Ammi ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace "Ba ki sha magani ba jiya da daddare ko daughter" ta nuna ma Ammi magungunanta a side drawer tace "Na sha Ammi" saketa Ammi tayi ta mike ta shiga bathroom ta hada mata ruwan wanka ta fito tace "Toh shiga kiyi wanka sai ki kara shan maganin" da taimakon Ammi ta sauka kan gadon, Ammi na rike da ita suka shiga bathroom, bayan ta wanke baki Ammi ta taimaketa tayi wanka ta fito, barin ta tayi ta sa kaya ta tafi hado mata shayi, Daddy na xaune parlor yana dube dube a laptop, ta tsaya bayan kujerar tace "Yallabai jikin imaan fa kar ya rikice mana ko xa aje asibiti tunda likitan ma baya nan" daddy ya mike yace "Bata jin dadi ne" Ammi tace "Nima yanxu na shiga ganin bata fito ba, her temperature is high tace bata yi bacci ba" daddy ya d'an yi shiru, Ammi tace "Kwanakin baya ciwon ya lafa sosai, as from some weeks ago yanxu duk sai ya tasar mata ga xaxxabi da ciwon kai kuma tana shan drugs dinta" Daddy yace "Toh ta shirya mu tafi asibiti" Ammi tace "Toh" komawa yayi ya xauna, ita kuma ta wuce dinning don hada mata shayi. Kwance ta sameta bayan ta sa abayar da ta fiddo mata, da kyar Imaan ta sha shayin, Ammi ta fesa mata turarrukan ta ta bata veil din abayar sannan suka fito parlor, kwanciya tayi kan kujera tana gaida daddy dake rike da makullin mota yana jiransu, ya amsa yace "Sannu mamana, tashi mu je to" mikewa tayi ya kama hannunta suka nufi kofa Ammi na masu Allah ya kiyaye hanya, A hanya daddy ya hadu da Abba ya taho daga part din Inna, gaisawa suka yi, Imaan ma ta gaishesa a hankali, Abba yace "Jikin ne ya tasar mata?" Daddy yace "Wllh kuwa, xa mu je asibiti ne yanxu" Abba yace "Subhanallah tana shan magunguna kuwa" Daddy yace "I think so" Abba yace "Toh likitan ta fa?" Daddy yace "Yayi tafiya ne" Abba yace "Toh tunda Muhammad na nan ba sai ya dinga dubata ba kafin likitan nata ya dawo, ko gwara a tafi asibitin?" Daddy yace "Noo in xai dubata shikenan, dama don likitan baya nan ne xa mu je asibitin" Abba yace "Let me give him a call, na barsa sashin inna, idan ma asibitin xa a sai ya kai ta kawai" Yana kokarin kiran Mujaheed suka hangosa yana tahowa, Abba ya maida wayarsa, har Mujaheed ya isa parking space da suke tsaye kallonsu kawai yake, Ya risina ya gaida Daddy, ya amsa masa da fara'a, Abba yace "Imaan xaka duba Mujaheed, bata jin dadi" Sosai gabansa ya fadi ya kalli Imaan dake jingine da mota duk ta wani langwabe.
I appreciate my fan's love always, ina yinku fisabilillah😘😍

spirimtanu Chase Hicks https://wakelet.com/wake/AW-sAZxFQaIU0dnPrLiB4
ReplyDeleterirelingcrem